Jamus ta nemi haɗin kan ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro
October 16, 2012Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi ƙira da a samu ƙarfafa haɗin kai da tuntuɓar juna tsakanin ƙasashen dake amfani da kuɗin euro. Merkel ta yi wannan kiran kwanaki biyu gabanin taron ƙolin shugabannin ƙasashen da ke amfani da kiɗin euro. Da take jawabi tare da baƙonta firimiyan ƙasar Sweden Fredrik Reinfeldt, wanda yace yana duba yiwuwar shigar da ƙasashen da basa amfani da takardar kudin euro, su shiga shirin Merkel keutata hada-jhadar bankuna, inda za su haɗa hannu bisa tsarin tafiyar da bankuna.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mouhamad Awal