1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar kulle ta fara aiki a Jamus

November 2, 2020

Dokar kulle ta makwanni 4 ta fara aiki gadan-gadan a Jamus kamar yadda mahukuntan kasar suka tsara, biyo bayan karuwar masu kamuwa da annobar corona ko COVID-19.

https://p.dw.com/p/3klSZ
Deutschland Merkel Regierungserklärung Coronavirus Bundestag
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

 

Sai dai a wannan karon dokar za ta kasance 'yar kwarya-kwarya, inda shagunan cin abinci da na sayar da barasa da kuma Sinima-sinima za su kasance a bude.

Haka zalika makarantu da gidajen rainon yara da kuma shagunan aski da gyaran gashi su ma za su cigaba da harkokinsu, amma bisa tsauraran matakai.

Kasar Jamus din dai ta taba shiga irin wannan halin a watannin Maris da Aprilun wannan shekarar da muke ciki. Yanzu haka dai wasu kasashen Turai da suka hada da Ostiriya da Faransa da Ireland suka fara daukar mataki yaki da dawowar cutar, inda Birtaniya ke shirin fara aiki da dokar kullen daga ranar Alhamis mai zuwa.