Jamus ta sallami jakadiyar Chadi dake kasarta
April 11, 2023Talla
A ranar Juma'ar da ta gabata ce mahukuntan na Ndjemena suka bai wa jakadan Jamus Gordon Kircke sa'o'i 48 na ya bar kasar bisa zarginsa da rashin mutunta dokokin diplomasiyya.
Matakin da ya janyo daukar martani baiwa jakadiyar Chadi Mariam Ali Moussa kwanaki biyu na ta tatara inata-inata ta bar kasar.
A wata sanarwar da ma'aikatar harkokin kasashen ketaren Jamus ta wallafa a shafinta ta Twitter, ta bayyana takaicin korar jakadanta inda ta ce yana gudanar da aikinsa bil hakki da gaskiya.
Sanarwar ta kara da cewar za su ci gaba da tattaunawa da bangarorin biyu kuma har yanzu suna da sauran wasu kananan jam'ian diplomasiyyar su a kasar ta Chadi.