Jamus ba zata sayar wa Turkiyya makamai ba
October 12, 2019Talla
Tun a farkon fara kai hari a yankin Arewacin Siriya Jamus da sauran takwarorinta sun yi Allah wadai da wannan mataki da Turkiya ta dauka.
A shekarar da ta gabata Jamus ta sayarwa da Turkiyya makamai da kudinsu ya kai miliyan dari biyu da arba'in da uku euro, kusan kashi daya daga cikin uku na cinikin makaman da ta yi na kimanin miliyan dari bakwai da sba'in da daya ana euro.
Hakazalika a farkon shekarar nan ma Turkiya da ke zama babbar mai cinikinta a kungiyar tsaro ta NATO, Jamus din ta saida mata da makamai na sama da miliyan 180 na euros.
Jamus dai na daga cikin manyan kasashen duniya kamar Amirka da Birtaniya da Faransa da Rushiya da kuma China da ke fidda makamai zuwa kasashen ketare.