1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta sanya dokar gwajin corona kafin shiga kasar

Binta Aliyu Zurmi
March 25, 2021

Ministan kiwon lafiya na Jamus Jens Spahn ya ce daga ranar Lahadi, duk wani matafiyi da ke shiga kasar sai ya nuna sakamakon gwaji da ke tabbatar da cewar ba ya dauke da kwayar cutar corona da bai wuce sa'o'i 48 ba.

https://p.dw.com/p/3rCBV
Coronavirus - Spahn zum Impfstoff Astrazeneca
Hoto: Annegret Hilse/REUTERS

Ministan kiwon lafiya Spahn ya ce sun riga sun umurci duk kamfanonin jiragen da ke jigilar al'umma da kar su yadda su dauki wani fasinja da ba shi da takardar da ke nuna ya yi gwajin corona. Wannan sabuwar dokar dai za ta yi aiki har watan Mayun da ke tafe.

A baya dai wannan doka na a kan matafiyan da ke fitowa daga kasashen da Jamus din ta kira masu hadari, amma yanzu dokar ta shafi kowa da kowa.

Wannan doka ba ta shafi masu shiga kasar ta mota daga kasashen Turai ba ko kuma wasu hanyoyi daban wanda suma akwai tasu dokar da aka tanadar musu.