1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Corona: Jamus ta ayyana dokar kulle mai karfi

December 13, 2020

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta umurci a rufe duk wani shagon da kasuwancinsa bai zama wajibi ba a fadin kasar don yakin kwayar cutar corona da ke ci gaba da bazuwa a kasar .

https://p.dw.com/p/3meaJ
Deutschland Covid-19 | PK im Bundeskanzleramt Merkel
Hoto: Rainer Keuenhof/Getty Images

Wannan na daya daga cikin abubuwan da sabuwar dokar kullen da jihohin kasar suka amince da ita a wannan Lahadin ta kunsa.
Sauran ka'idojin sun hada da; haramta wa mutane shan barasa a bainar jama'a, an umurci makarantu da su rufe, idan kuma ya zama dole su yi aiki to su koma ta intanet, kuma su tsawaita hutun Kirsimeti da sabuwar shekara ga dalibai har zuwa 10 ga watan Janairu.

Kazalika hukumomi sun umurci a kulle shagunan aski da gyaran gashi. To amma duk da haka Jamus din ta ce ta amince masallatai da coci-coci su bude indai za su bi matakan kariya, sannan iyalai za su iya kai wa junansu ziyarar da ta kunshi mutanen da ba su haura biyar ba.


Yawaitar corona a Jamus ce dai ta tilasta wa gwamnati daukar wannan mataki, a cewar Angela Merkel. Ana sa ran sabuwar dokar kullen ta fara aiki daga ranar Laraba zuwa ranar 10 ga watan Janairu mai kamawa.