Jamus ta soki Amurka kan rikicin Yukren
February 7, 2014Talla
Mai magana da yawun Merkel din ta ce kalaman da Victoria Nuland, jami'ar diflomasiyyar Amurka da ke kula da lamuran Turai ta yi game da kungiyar ta EU abu ne da sam ba za su amince da shi ba.
An dai jiyo wani fafai na sautin muryar da ke kama da ta Ms. Nuland din na cewar kyautuwa ya yi a yi watsi da duk irin matsayin da kungiyar EU din ta dauka kan kasar ta Yukren baya ga zagin da aka ce an ji a kalaman nata.
Wannan dai ya sanya mai magana da yawun Merkel din cewar fitar wadanan kalamai marasa dadi wata 'yar manuniya ce da ke tabbatar da irin aiki na gari da kantomar harkokin wajen kungiyar EU Catherine Ashton ke yi na kokarin sulhunta gwamnatin Yukren din da 'yan adawa.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita Umaru Aliyu