Jamus ta taka rawa wajen musayar fursunoni da Rasha
August 2, 2024Babban jigo a musayar fursunoni da ya hada kasashe da dama shi ne Vadim Krasikov, dan Rasha da aka yanke wa hukuncin zaman kaso bisa samunsa da kisan wani tsohon dan gwagwarmayar Chechenya a Berlin a shekarar 2019.
Rasha ta gabatar da tayin musayar fursunonin ga Amurka a 2022 domin sako mata Krasikov wanda ke zaman daurin rai da rai a Jamus. Sai dai saboda Krasikov ba dan asalin Amurka ba ne, Jami'an Amurka basu bai wa tayin wani muhimmanci ba.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya fada a kwanan nan a cikin wani shirin talabijin na Tucker Carlson cewa a shirye shirye ya ke domin musayar fursunonin da Krasikov.
Shawarar sakin Krasikov dai batu ne na siyasa mai sarkakiya ga Jamus, bisa la'akari da girman laifin kisan wanda ya auku da rana tsaka a wani dandali a kusa da majalisar dokoki da kuma ofishin shugaban gwamnatin Jamus a Berlin