Jamus ta ware biliyoyi don rage radadin rayuwa
September 5, 2022Talla
Sanarwa wannan aniyar dai ta zo ne bayan matakin da Rasha ta dauka na katse samar da makamashin iskar gas ta bututun nan na Nord Stream 1 wanda ke sama wa kasashen Turai makamashin.
Tsarin rage radadin karo na uku, zai hada da rage wa mutane kudin tikitin tafiye-tafiye da na wuta da iskar gas ga 'yan fansho da dalibai da ma sassauta wa kamfanoni da ke cin makamashi sosai.
Watanni ukun da suka gabata ne dai gwamnatin Jamus din ta sanar da rangwamen tikitin zirga-zirga zuwa ko'ina na kasar zuwa euro tara a wata.
Yanzu kasar ta kintsa wa samar da wadatacciyar gas da mutane za su iya amfani da ita lokacin sanyi na hunturu da ke tafe, domin kauce wa yankewar wuta da ayyukan na'urorin dumama gidaje da wuraren aiki.