1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta zargi Jamus da wuce gona da iri

August 1, 2020

Jamus ta dakatar da yarjejeniyar shari'a da ke a tsakaninta da China, bayan yankin Hong Kong ya sanar da dage zaben 'yan majalisar dokoki.

https://p.dw.com/p/3gG7G
Deutschland Berlin | Wang Yi, Außenminister China & Angela Merkel, Bundeskanzlerin
Hoto: picture-alliance/Xinhua News Agency/W. Qing

Ministan Harkokin Wajen Jamus Heiko Maas ya ce sun dauki wannan mataki ne domin mahukumtan yankin Hong Kong sun hana wasu 'yan takara 12 masu adawa da gwamnati shiga zaben, ga shi kuma uwa-uba sun dage zaben da aka shirya gudanarwa a watan gobe na Satumba zuwa shekara mai zuwa, abin da ya saba wa tanadin dokoki na kasa da kasa.

Sai dai ofishin jakadancin China da ke Jamus ya ce bai ji dadin matakin da Jamus ta dauka na dakatar da yarjejeniyar kama masu laifuka da ke a tsakanin kasashen biyu ba, yana mai cewa abin da Jamus ta yi ya saba wa ka'ida kuma China za ta mayar da martanin da ya dace.


Tun kafin yanzu dai Jamus da wasu kasashen Turai sun sanya takunkumin sayar wa da yankin Hong Kong duk wani abu da ake ganin za a iya amfani da shi wurin cutar da masu kin jinin gwamnati. Tuni da ma kasashen Birtaniy a da Canada New Zealand da Ostiriya suka yanke alakarsu da China ta fuskar shari'a.