COVID-19: Jamus ta zama abar koyi
May 7, 2020Duk da asarar rayukan da aka samu a Jamus din dai, kasar ta yi kokari wajen dakile yawan wadanda suka kamu da kuma wadanda cutar ta yi ajalinsu. An samu sauki matuka fiye da yadda lamarin yake a wasu kasashen duniya.
Mutane da dama sun warke
Mutane kusan dubu 170 ne dai ya zuwa yanzu aka tabbatar sun kamu da wannan cuta ta coronavirus a Jamus, kuma bisa ga alkaluman da hukumomi suka bayar mutum kusan dubu 140 daga cikin wanda suka kamu sun warke, yayin da ta halaka mutum kimanin dubu bakwai, wanda hakan ke nuna cewar wadanda ke dauke da wannan larura a halin yanzu ba su wuce su dubu 20 da 'yan doriya ba.
Yawan wadanda suka warke din da ma karancin wadanda cutar ta yi ajalinsu, abu ne da ya dauki hankulan al'umma a kasar da sauran sassan duniya, musamman idan aka kwatanta da kasashekamar Spian da Italiya da kuma Birtaniya.
Ina sirrin yake?
Wannan ya sanya da dama aza ayar tambaya kan irin matakan da Jamus din ta dauka wajen cimma wannan nasarar. Lothar Wieler shi ne shugaban cibiyar nan ta Robert Koch Institute da ke sanya idanu kan cututtuka masu saurin yaduwa. A hirarsa da DW, Wieler ya ce daukar matakai cikin gaggawa da suka yi bayan bullar cutar shi ne sirrin nasarar da kasar ta samu.
Wani abu har wa yau da ya taimakawa kasar wajen fiddawa kanta kitse daga wuta shi ne, yin gwaje-gwaje da yawa domin tantance masu dauke da cutar da kuma samar da kayan aiki na kula da majinyata a sakuna da lungunan kasar kamar yadda Lothar Wieler ya nunar, inda ya kara da cewar hukumi a kasar sun dauki wannan bangare da muhimmancin gaske.
Tsayayyar shugaba
Baya ga batu na samar da kayan aiki, wani abu da ya taimakawa kasar shi ne irin yadda shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel ta yi tsayin daka wajen ganin tinkarar matsalar, inda ta rika aiki kafada da kafa da gwamnonin jihohin kasar 16. Wannan yunkuri na Merkel din, ya sanya ta yi fice a tsakanin takwarorinta wajen yaki da cutar musamman ma idan aka kwatanta da irin tafarki da wasu shugabanni na duniya suka dauka na yin sako-sako da batun, ciki kuwa har da Jair Bolsonaro na Brazil da Donald Trump na Amirka.