Jamus ta yi kira da a aiwatar da sauye sauyen siyasa a Aljeriya
January 7, 2012Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya isa ƙasar Aljeriya da ke zama zangon farko na rangandin kwanaki huɗu da zai gudanar a wasu ƙasashe na arewacin Afirka. A lokacin da ya ke bayani bayan da ya gana da takwaran aikansa na Aljeriya Mourad Medelci, Westerwelle ya yi kira ga hukumomin Algers da su aiwatar da sauye sauyen da suka dace. kana ministan na Jamus ya bayyana farin cikinsa game da amincewa da Aljeriya ta yi da buɗe wa 'yan kallo na ƙetare ƙofofita, domin su je su sa ido a zaɓɓukan gama gari da za su gudanar a watan Afirilu mai zuwa.
Westerwelle zai gana nan gaba da firaministan Aljeriya Ahmed Ouyahia, da kuma ministan masana'antu da ma dai 'yan kasuwan ƙasar, kafin ya zarce zuwa ƙasashen Libya da kuma Tunisiya. Ministan harkokin wajen na Jamus na wannan ziyarar aikin ne, da nufin kyautata dangantakar cinikayya tsakanin ƙasarsa da kuma ƙasashen na arewacin Afirka, tare da nuna musu goyon baya ga yunƙurin da suke yi na tabbatar da wanzuwar demokaraɗiya a cikinsu.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdullahi Tanko Bala