Jamus ta yi kira ga Isra'ila kan hakkin 'dan adam a Gaza
February 26, 2024Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta bukaci Isra'ila da ta bi tanade-tanaden dokokin kare hakkin 'dan adam na kasa-da-kasa a yakin da take yi a Gaza, wajen kare rayukan fararen hula.
Karin bayani:Matsayar Jamus a rikicin Isra'ila da Hamas
Annalena Baerbock ta bayyana hakan ne a birnin Geneva na Switzerland, yayin taron hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, inda ta ce Isra'ila na da 'yancin kare kanta kamar ko wace kasa a duniya, amma kuma wajibi ne ta kula da ka'idojin da ke shimfide na hakkokin jama'a, la'akari da yadda ake ganin kananan yara cikin yunwa a galabaice suna gararamba ko takalma babu a kafarsu suna kuka, wasu iyaye mata na gudu cikin firgici rike da yara, bayan rushe musu gidajen.
Karin bayani:Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya gana da shugaba Xi Jinping na Chaina kan Gaza
Haka zalika ministar ta Jamus ta yi kira da kwamitin da ya bibiyi batun take hakkin 'dan adam da kasar Iran ke aikatawa, musamman wajen dakile masu zanga-zanga.