Jamus ta yi kiran a dakatar da rikicin Isra'ila da Hezbollah
September 27, 2024Ministar hakokin wajen Jamus, Annalena Baerbock ta shaida wa taron Majalisar Dinkin Duniya, cewar fadadar rikicin da ake gani a yankin Gabas ta Tsakiya ba za ta kawo wata masalaha ba ta fuskar tsaro.
Babbar jami'ar diflomasiyyar ta Jamus dai na daga cikin wadanda ke neman ganin an cimma tsagaita wuta a rikicin da ya kunno kai tsakanin Isra'ila da kungiyar Hebolaah ta kasar Labanan.
A cewar Baerbock, dukkanin bangarorin da ke fada a Gabas ta Tsakiya dai na bukatar zaman lafiya mai dorewa.
Ita ma Majalisar Dinkin Duniyar, ta koka da hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Labanan, a martanin da take kai wa Hezbollah.
Kimanin mutane 700 ne dai hare-haren Isra'ila suka yi ajalinsu a cikin wannan mako a Labanan din, kamar yadda ma'aikatar lafiyar kasar ta sanar.