Jamus ta yi tayin sasanta Rasha da Ukraine
November 27, 2018Talla
Shugabar gwamnati Angela Merkel da 'yan majalisar dokokinta sun yi roko ga bangarorin biyu na Ukraine da Rasha su sassauta tada jijiyoyin wuya a daidai lokacin da Ukraine ta nemi taimakon soji daga Jamus da kuma NATO.
A ranar Litinin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tattauna ta wayar tarho da shugaban Rasha Vladimir Putin kan bukatar kwantar da hankula kamar ydda ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya nunar.
" Yace shugaba Putin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun tattauna ta wayar tarho game da halin da ake ciki. Sun kuma cimma wata fahimta wanda nake tsammani za a aiwatar nan ba da jimawa ba".