Jamus: Tallafin makamai ga kasar Ukraine
December 27, 2022Gwamnatin Jamus ta ba da sahalewar sayar da makamai da kudinsu ya kai kimanin euro biliyan tara wanda ke zama cinikin makamai na biyu mafi girma da kasar ta gudanar a shekarar 2022 a cewar ministan tattalin arzikin kasa Robert Habeck
Fiye da kashi daya cikin kashi hudu na makaman an tura su ne zuwa kasar Ukraine a yayin da take kokarin kwatar kanta daga mamayar da Rasha ta yi mata.
Jam'iyyun kawancen gwamnatin Jamus dai sun bukaci rage sayar da makamai ga kasashen waje bayan da suka hau karagar mulki, to sai dai sun sauya matsaya bayan da Rasha ta mamaye Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu kamar yadda shugaban gwamnati Olaf Scholz ya sanar bayan da gwamnatin ta fuskanci kakkausar suka tun da farko na kin taimaka wa Ukraine da manyan makaman yaki.
Gwamnaatin Jamus din ta talla wa Ukraine da makamai da kudinsu ya haura euro biliyan biyu da miliyan dari biyu da arba'in.