1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafawa kasashen Afirka yaki da yunwa

Abdoulaye Mamane Amadou
June 17, 2020

Gwamnatin Jamus ta ware makudan kudade don agazawa wasu kasashen Afirka masu fama da matsalar yunwa shawo kan matsalar a daidai lokacin da matsalar yunwar ke dada yin kamari a kasashen

https://p.dw.com/p/3dvNE
Deutschland Berlin | Bundeskabinett | Angela Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Hanschke

Jamus zata tallafawa wasu kasashen yammacin Afirka biyar yaki da matsalar fari da karancin abinci, sakamakon matsalar yunwa da al'ummomin kasashen suka tsunduma a ciki tun bayan bullar annobar corona.

Da yake magana kan batun a yayin wata hira da jaridar "Rheinische Post" ministan raya kasashe na tarayyar Jamus Gerd Müller, ya ce Jamus za ta samar da tsabar kudi euro miliyan 19 a matsayin tallafi ga kasashen Mali Burkina Faso da Murtaniya da Senegal, inda manoman kasashen za su iya amfani da su don tunkarar bala'in yunwar da ta kunno kai, tare da samun tabbacin abinci mai dorewa ga iyalai, haka da samun wadataccen irin noma da cimakar dabobinsu, idan har daminar bana ta zo wa al'ummomin kasashen da gardama.