1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimako wajen yakar corona

Zainab Mohammed Abubakar
May 29, 2021

Gwamnatin Jamus za ta taimaka wa Afirka ta Kudu da miliyoyin allurar rigakafin cutar corona, a ta bakin ministan lafiya Jens Spahn da ke ziyara a birnin Johannesburg.

https://p.dw.com/p/3u9di
Südafrika Corona-Gesprächen | Besuch von Bundesgesundheitsminister Spahn
Hoto: Christoph Soeder/dpa/picture alliance

Spahn ya ce Berlin na shirye wajen bada gudunmowar allurai na kwatankwacin dalar Amurka miliyan 61, a jawabin da yayi a jami'ar birnin  Johannesburg, inda ya ce Jamus na dokin bada tallafin fasaha, kamar Faransa da kungiyar Tarayyar Turai.

Jamus da sauran kasashen Turai dai sun yi adawa da tattauna batun jingine hakkin mallaka na fasahar hada rigakafin cutar COVID 19 da wasu kamfanoni suka samar, kan cewar yin haka zai kashe gwiwar kamfanoni masu zaman kansu yin bincike na gaba, kan wata allurar rigakafi makamanciyar ta coronavirus.

A nashi bangaren shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bukaci adalci da gaskiya dangane da tallafin allurar rigakafin da ake bai wa kasashe matalauta, musamman ta fannin farashin alluran.