Jamus: 'Yan jam'iyyar SPD sun soma zabe
February 20, 2018Sai dai wani binciken jin ra'ayin jama'a da aka fitar a wannan Talatar, ya nunar cewa jam'iyyar da ke da tsattsauran ra'ayi na kyamar baki ta AFD ta shiga gaban jam'iyyar ta SPD da yawan wadanda ke bukatar kada mata kuri'a. Mambobi 464.000 na jam'iyyar ta SPD za su yi zaben ne ko ta hanyar aikewa da wasika, ko kuma ta shafin Internet domin nuna amincewarsu ko akasin haka kan batun kafa sabuwar gwamnatin hadaka tare da jam'iyyar shugabar gwamnatin ta Jamus ta CDU da abokiyar kawancenta ta kullum CSU.
A ranar 04 ga watan Maris mai zuwa ne dai ake sa ran samun sakamaon zaben wanda ke da babban mahimmanci ga shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel wadda ta samu karamin rinjaye a zaben da ya gudana na 'yan majalisar dokoki na 24 ga watan Satumban bara.