1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yiwuwar karin kyamar baki a Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 25, 2022

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi gargadin sabuwar barazana daga masu tsattsauran ra'ayin kyamar baki, a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru 30 bayan kai harin wariyar launin fata mafi muni a kasar.

https://p.dw.com/p/4G3tI
Deutschland | Rostock-Lichtenhagen | Gedenkveranstaltung | Bundespräsident Steinmeier
Zoyarar shugaba kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier wajen kisan wariyar launin fataHoto: Jens Büttner/dpa/picture alliance

Shugaban kasar ta Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana hakan ne a birnin Rostock da ke arewacin kasar, yayin tunawa da harin wariyar launin fatar da ya afku a shekara ta 1992 yayin da wasu dubban mutane suka rika kuwwa da tafi ga wani mahari da ya farmaki gidan ajiye masu neman mafaka. Ya kara da cewa Jamus ta gaza kawo karshen kiyayya da tsattsauran ra'ayin kyamar baki tsawon shekaru, a daidai lokacin da 'yan siyasa ke gargadin yiwuwar samun 'yan tawaye a lokacin sanyin hunturu a bana sakamakon tsadar makamashi da hauhawar farashi da kuma matakan yaki da annobar corona.