1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Za a ci gaba da rike Puigdemont

Yusuf Bala Nayaya
March 26, 2018

An dai kama tsohon shugaban na yankin Kataloniya bisa sammaci da ke kansa a Spain, kasancewar na kan gaba wajen yi wa mahukunta tawaye da neman yankin ya balle daga kasar ta Spain.

https://p.dw.com/p/2v2CV
Carles Puigdemont
Hoto: Reuters/Lehtikuva/M. Kainulainen

Wata kotu a Neumünster a jihar ta Schleswig-Holstein a Jamus a ranar Litinin ta bayar da umarnin ci gaba da rike Carles Puigdemont tsohon shugaban yankin Kataloniya, matakin da ke zama share hanya wajen mayar da shi kasarsa ta Spain.

Jamus ta bayyana a wannan rana ta Litinin cewa batun mayar da tsohon shugaban yankin Kataloniya Puigdemont, da aka tsare shi a jihar ta Schleswig-Holstein da ke arewaci na Jamus a ranar Lahadi, batu ne da ke a hannun kotun yankin.

Mai magana da yawun gwamnati Steffen Seibert ya ce lamarin ana duba shi kamar yadda doka ta tanada a Jamus da ma batun sammaci a tsakanin kasashen na Turai, ya ce takaddamar za a warwareta ne kawai ta hanyar dokar da kasar ta Spain ta tanada.