1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta farar COVID allura wa kowa

Zainab Mohammed Abubakar
March 10, 2021

Kungiyar kwarraru a fannin lafiya na fatan ganin ingantuwar yi wa mutane allurar rigakafin corona da ake shirin farawa a watan Afrilu gadan gadan a fadin Jamus.

https://p.dw.com/p/3qSGq
Tschechien Brno | Impfzentrum
Hoto: Vaclav Salek/Ctk/dpa/picture alliance

Shugaban kungiyar likitocin asibitocin sha-ka-tafi na Jamus Adreas Gassen, ya shaidar da cewar kama daga watan Afrilu, asibitocin za su iya yi wa mutane miliyan 20 allurar rigakafin corona.

Furucin nasa na zuwa ne gabannin wata ganawa tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi kan lokacin da ya dace likitocin su fara yi wa mutane allurar rigakafin na COVID 19. A watan Afrilu ne dai ake saran za su fara.

Mr Gassen ya ce ana saran yi wa dukkan mutane zangon farko na allurar nan da tsakiyar watan Yuni, kana a kammala yi wa kowa da kowa nan da watan Augusta. Ya soki gwamnati kan rashin sanya likitocin cikin tsarin yin allurar tun da farko.