1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta ba wa Ukraine karin makamai

Mouhamadou Awal Balarabe
July 11, 2023

Ma'aikatar tsaron Jamus ta bayyana cewar za ta kashe kusan Euro miliyan 700 don kara yawan makamai da take bai wa kasar Ukraine da ke fama da yaki, a lokacin da NATO ke taron koli a birnin Vilnius.

https://p.dw.com/p/4Tiwo
Irin manyan makamai da Jamus za ta ba wa UkraineHoto: Philipp Schulze/dpa/picture alliance

Wannan sanarwar ta zo ne a ranar farko na taron kolin shugabannin NATO a Vilnius na Lithuaniya. Ita dai Berlin da ke a sahu na biyu na masu ba da taimakon soji ga Ukraine bayan Amirka, za ta bayar da na'urorin Patriot don dakile yiwuwar harin makami mai linzami da motocin sulke 40 da tankunan yaki da kuma manyan bindigogi 20,000.

Kunshin makamai na karshe na Jamus ta ba wa Ukraine ya kasance na ranar 13 ga Mayu. Ita dai Jamus ta dade tana shan suka daga Kiev da wasu kawayenta na Turai, dangane da jan kafa wajen gudunmawar makamai da take baiwa Ukraine. Amma a watannin baya-bayannan, Berlin ta kara himma inda take bayar da harsasai da tankunan yaki.