1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin ceto kamfanin jirage na Lufthansa

Gazali Abdou Tasawa
May 21, 2020

Gwamnatin Jamus na shirin kaddamar da wani shirin tallafin kudi ga kamfanin jiragen saman kasar na Lufthansa wanda ke fuskantar barazanar durkushewa a sakamakon annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3cZYB
Deutschland Bundesregierung plant offenbar Direkteinstieg bei Lufthansa
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Roessler

Kamfanin jiragen sama na Lufthansa na kasar Jamus ya ce gwamnatin kasar na gab da ceto shi daga barazanar durkushewa a sakamakon wani shirin tallafin kudi miliyan dubu tara na Euro da gwamnatin Berlin ke shirin kaddamarwa.

A wata sanarwa da ya fitar a wannan Alhamis kamfanin na Lufthansa ya ce kawo yanzu ba a kai ga karkare shirin ba wanda bankin zuba jari na kasar ta Jamus wato KfW zai aiwatar da shi.

Shirin ya tanadi tallafin kudi miliyan dubu tara daga cikin miliyan dubu uku a matsayin bashi. Aiwatar da shirin zai bai wa gwamnatin kasar ta Jamus damar mallakar kaso 25 daga cikin dari na hannun jarin kamfanin.

 A shekara ta 1997 ne dai gwamnatin kasar ta Jamus ta sayar da kamfanin jiragen saman na Lufthansa ga 'yan kasuwa. Amma kuma a yanzu ya kama hanyar durkushewa a sakamakon annobar Coronavirus. Lamarin da ya kai gwamnatin ga daukar matakin ceto shi ta hanyar zuba jari a cikinsa.