SiyasaJamus
Jamus za ta dauki 'yan gudun hijirar Ukraine
March 6, 2022Talla
Jamus ta sanar da cewa za ta karbi 'yan gudun hijira daga kasar Ukraine. Ministar harkokin cikin gida Nancy Faeser ce ta sanar da haka a cikin wata tattaunawa da ta yi da jaridar Jamus ta mako-mako da ke fita ranar Lahadi ta Bild am Sonntag.
Ministar ta ce Jamus na son ceto rayukan mutanen da ke neman taimako, a don haka za ta karbi duk mutumin da ya fito daga Ukraine ko da kuwa ba dan kasar ta Ukraine ba ne.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane miliyan daya ne suka tsere daga Ukraine domin guje wa tashin hankalin da ya biyo bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.