Jamus za ta karfafa dangantaka da Amirka
November 9, 2020Talla
Wannan dai shi ne martanin farko na shugabar gwamnatin kan sakamakon zaben Amirkar bayan sakon taya murna da ta aike wa zababben shugaban kasar Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris a karshen mako.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu dai ta yi tsami a shekaru hudu na mulkin shugaba Donald Trump. A wani matakin da ake ganin na kuntatawa ga Jamus game da kason gudunmawar kudi ta fuskar tsaro, shugaba Trump ya janye dubban sojin Amirka a sansanonin Jamus, sai dai kuma za a sa ido a gani ko Biden zai sauya matakin.
Merkel da sauran shugabannin Jamus na fatan inganta tuntubar juna da karfafa hadin gwiwa da Washington karkashin gwamnatin Biden.