1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar gwamnatin Jamus za ta karfafa tattalin arziki

Suleiman Babayo AH
December 15, 2021

Sabon gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi jawabin farko a gaban majalisar dokoki inda ya bayyana shirin karfafa tattalin arzikin kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/44Ibj
Bundeskanzler Scholz, erste Regierungserklärung im Bundestag
Hoto: Kay Nietfeld/picture alliance/dpa

Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz ya ce gwamnatinsa za ta karfafa tattalin arzikin kasashen Turai da saka jari kan tattalin arziki mai muradun kare yanayin duniya.

Sabon shugaban gwamnatin ya yi jawabi a karon farko a gaban majalisar dokokin kasar ta Bundestag tun bayan da ya dauki madafun iko a makon jiya daga hannun tsohuwar shugabar gwamnati Angela Merkel. A cewar sabon shugaban gwamnatin ta Jamus, Olaf Scholz  zai ci gaba da karfafa tattalin arziki da Jamus da magance matsalolin masu nasaba da annobar da ake fuskanta.

Olaf Scholz sabon shugaban gwamnatin mai shekaru 63 da haihuwa ya ce samun nasarar Tarayyar Turai shi ne mizanin samun ci-gaban Jamus.