1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a sasauta dokar zaman gida a Jamus

Binta Aliyu Zurmi
May 6, 2020

Mahukunta a Jamus na shirin sasauta dokar hana zirga-zirga a fadin kasar, sai dai za a ci gaba da sa ido sosai domin ganin ba a sami barkewar sabbin kamuwa da kwayar cutar ba.

https://p.dw.com/p/3bqHc
Deutschland Coronavirus (COVID-19) Testzentrum in Frankfurt
Hoto: Reuters/K. Pfaffenbach

Hukumar da ke kula da cututuka masu yaduwa ta kasar ta ce akwai yiwuwar sake samun barkewar cutar a mataki na biyu harma zuwa na uku.

A wannan rana ta Laraba ce ake sa ran shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shuwagabannin jihohi goma sha shidda na kasar za su yi wani taro ta kafar bidiyo domin amincewa da matakin sassauta zirga zirgar.

Har yanzu dai gwamnatin Jamus na son ganin an ci gaba da dokar haramta taron jama'a da suka wuce mutum biyu da kuma dakatar da wasanni har zuwa karshen watan Augusta. Gwamnatin ta amince da bude dukkan shagunna karkashin tsauraran matakan tsabtan da kuma barin tazara tsakanin mutane.

Da safiyar yau, cibiyar kula da cututuka ta Jamus, Robert Kock ta tabatar da karuwar mutum 947 da suka kamu da cutar ta COVID 19.