1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba za a tsananta kulle a Easter ba - Merkel

Abdul-raheem Hassan
March 24, 2021

Gwamnatin Jamus za ta janye tsauraran matakan yaki da corona da ta ayyana a lokacin bikin Easter, bayan da matakan suka gamu da fushin jama'a.

https://p.dw.com/p/3r3Nc
Berlin Kanzlerin Merkel vor Kabinettssitzung
Hoto: picture alliance/dpa/dpa-Pool

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce za ta janye matakin farko da gwamnati ta dauka, na tsauarara dokar sake kulle kasar a lokacin hutun bikin Easter saboda yaki da annobar corona. Shugabar ta ce akwai kuskure a matakan saboda ba za su yiwu ba a zahiri.

Dama dai Jamus na shirin sake kulle shaguna da takaita haduwar jama'a daga ranar 1 ga watan Afirilu zuwa 5. Sai dai shugabannin masana'antu da 'yan kasuwa sun ce dokar ya bar su cikin duhu na sanin hakikanin abin da dokar ke nufi.