1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta saya wa Ukraine makamai

Ahmed Salisu
March 29, 2023

Gwamnati Jamus za ta bayar da tallafi na kayan yaki ga kasar Ukraine domin kara mata karfi wajen kare kanta a yakin da Rasha ke yi a kasarta.

https://p.dw.com/p/4PSnw
Deutschland | Leopard 2 Panzer | Strong Europe Tank Challenge in Grafenwöhr
Hoto: U.S. Army/ABACA/picture alliance

Kwamitin da ke kula harkokin kudi na majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ne ya sahalewa gwamnatin kasar ta kashe tsabar kudi har euro biliyan 8 don sayen makamai da nufin hannatasu ga Ukraine. 

Daga cikin irin kayan yakin da za a mayar da hankali wajen saye akwai tankokin yaki da motocin soji masu silke da kuma albarusai.

Da yake mayar da maratani kan matsayin da majalisar ta dauka, ministan tsaron Jamus Boris Pistorius cewa ya yi matakin wani babban ci gaba da ke nuna irin goyon bayan da Jamus ke ba wa Ukraine a yakin da take da Rasha.