1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta takaita mallakar bindiga

Abdul-raheem HassanJuly 24, 2016

Manyan jami'an gwamnatin kasar Jamus, sun nemi da tsaurara dokokin mallakar bindiga da wasu muggan makamai da ke barazana ga rayuwar al'umma.

https://p.dw.com/p/1JVAP
Deutschland Bundestag Armenienresolution Abstimmung
Hoto: Getty Images/AFP/O. Andersen

Jami'an gwamnatin kasar Jamus sun yi kira da a waiwayi dokokin mallakan bindiga, wannan bukata dai na zuwa ne bayan harin da wani matashi mai shekaru 18 ya kai a rukunin kantuna a birnin Munich ranar jumma'ar da ta gabata wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum 9 nan take hada shi maharin 10. Mataimakin shugabar gwamnatin Jamus Sigma Gabriel, ya ce ya zama wajibi a tsaurara doka da zai takaita mallakar bindigogi da ma sauran muggan mukamai.

Hukumin tsaro suna zurfafa bincike dan gano yadda maharin mai fasfon kasashen Iran da Jamus ya mallaki samfurin wata bindiga mai tsawon milimita 9 dauke da da harsahi 17 da aka samu a dakinsa. Bayanai dai na kara bayyana cewa maharin ya dau tsawon shekara guda ya na shirya wannan harin.