1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Za ta tallafawa 'yan kasar Siriya da matsuguni

Binta Aliyu Zurmi MNA
January 24, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi na'am da bukatar tallafawa wadanda rikicin yaki ya daidaita a kasar Siriya da matsuguni bayan da takwaranta na Turkiyya ya baiyana damuwa kan halin da suke ciki.

https://p.dw.com/p/3WmvR
Türkei Bundeskanzlerin Merkel zu Besuch in Istanbul
Hoto: AFP/B. Kilic

Merkel ta fadi hakan ne a yayin da take jawabi a gaban manema labarai a ziyara da ta kai kasar Turkiyyan. A na shi bangaren, Erdogan ya ce akwai bukatar daukar matakin gaggawa ta la'akari da halin da dubban 'yan gudun hijirar suka sami kansu ciki a sakamakon barkewar rikici a yankin Idlib.

Ya dai baiyana fargaba a game da sakamakon da zai biyo baya na kwararar wadannan 'yan gudun hijira cikin kasar Turkiyya muddin ba a dauki matakin kulawa da su ba.

Fada ya kara barkewa a tsakanin rundunar gwamnatin Siriyar da ke biyayya ga Shugaba Bashar Al-Assad da 'yan tawayen da ke rike da ikon yankin na Idlib, tungar karshe da ta rage a hannun 'yan tawayen, lamari da ya kara asassa rikicin kasar na fiye da shekaru takwas.