1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta tattauna da jagororin Taliban

September 5, 2021

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce Jamus za ta tattauna da jagororin Taliban a Afghanistan game da 'yan Afghanistan da suka yi aiki da kungiyoyin kasar Jamus wadanda suka nuna fargabar zama a kasar.

https://p.dw.com/p/3zwq5
Nach Flutwelle | PK Laschet und Merkel
Hoto: Frank Ossenbrink/imago images

A wani jawabin da ta yi wa maneman labaru a birnin Hagen na nan Jamus, Angela Merkel ta ce babu wani zabin da ya wuce tattaunawa da shugabannin na Taliban, kasancewar su ne ke rike da kasar a yanzu.

Haka nan ma shugabar gwmanatin ta Jamus, ta ce lallai ne a kyale kugiyoyin agaji su ci gaba da taimaka wa mutanen da ke cikin mawuyacin hali a Afghansitan.

A ranar Juma'ar da ta gabata ma dai ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai, sun amince da wasu sharudan samar da kwarya-kwaryar hadin kai ga Taliban din na Afghansitan.