Jamus: Zaman karshe na kulla kawance
February 6, 2018A wannan Talatar ce ake sa ran Jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da SPD, za su kammala tattunawar kulla kawancen samar da gwamnatin hadaka, da ake ganin zata kawo karshen kiki-kakar siyasa da kasar da ta fi kowacce karfin arziki a nahiyar Turai ta shiga. Da misalin karfe goma na safiyar Talatar ne dai ake sa ran wakilan jam'iyya mai mulki ta CDU da CSU da kuma SPD za su yi ganawar da ake ganin ta karshe ce, bayan dogon turanci da aka sha jiya Litinin a kokarin da ake yi na cimma matsaya.
Manyan fannonin da aka sami tarnaki a zaman tattaunawar baya, su ne fannonin kudaden gudanar da harkokin kiwon lafiya da samar da ayyukan yi gami da na fannin tsaron kasa. Jami'an dai na bayyana fatar cimma kyakkyawar madafa a zaman da za a yi nan gaba a yau din.