Dalibai na zanga-zanga don kare muhalli a Jamus
April 26, 2019Masu yin wannan zanga-zangar sun yanke shawarar yin tattakin ne a duk mako don yin matsin lamba ga shugabannin Tarayyar Turai don ganin sun dau makatai na alkinta muhalli kasancewar matakan da suke dauka ba su wadatar ba a zahiri. Daliban na kauracewa duk wani karatu a irin wannan rana da suke kira Fridays for Future don daukar matakai kwakkwara ga muhalli. Wannan yunkuri da kashi 40 cikin 100 da daliban Jamus suke dauka na sanya bangarori da dama kasancewa cike da fatan ganin lamura sun sauya duba da matsin lamba da daliban suke wanda masana suka nuna cewa ya sha bam-bam da irin wanda aka saba gani a baya. Wasu daga cikin daliban ire-irensu Clara "ta ce fafutukar Fridays for Future ba ta da wata alaka da siyasa tana mai cewa abin da suke bukata shi ne yin gyare-gyare masu ma'ana game da batun na muhalli." ta na mai cewa Ba ma bukatar jinjina, abin da muke so shi ne a dauki mataki kwakkwara. A yanzu dai daliban basu da wata cikakkiyar amsa kan bukatarsu to amma kuma masharhanta na ganin kila su iya yin tasiri wajen samu sauyi musamman ma nan dan 'yan shekaru masu zuwa musamman idan suka samu shiga cikin harkoki na siyasa.