Jamusawa biyu sun yi wa Iran kutse
October 15, 2010Kafafen yaɗa labaru na gwamnatin Iran sun ba da rahotannin da ke nuni da cewa wasu Jamusawa biyu da aka kama a lokacin da suka yi ƙoƙarin yin fira da ɗan Sakineh Asthiani da aka yanke wa hukuncin kisa bisa laifin yin zina, sun amsa lafin shiga ƙasar ba da cikakkun takardu ba-abin da mahukuntan Iran suka ce babban laifi ne. Mahukuntan sun kuma zargi Jamusawan biyu da laifin yin hulɗa da tsageru masu nuna adawa da juyin- juya-halin ƙasar ta Iran da ke wajen ƙasar. Ma'aikatar harkokin Jamus da ke birnin Berlin ta buƙaci sakin mutanen biyu. Sai da ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle da takwaransa na Iran, Manoucher Mottaki suka tattauna game da wannan batu a daura da taron ministocin harkokin wajen Ƙungiyar Tarayar Turai da ya gudana a birnin Brussels na ƙasar Beljiyam inda ya bayyana imanin cewa Mottaki zai ɗauki mataki na gaban kansa game da wannan al'amari. A wani ci gaban kuma an samu daidaiton komawa ga teburin tattaunawa tsakanin gaggan ƙasashen duniya da Iran akan shirinta na nukiliya, bayan da a yau ɗin nan Iran ta amince da tayin da aka yi mata na komawa ga teburin tattaunawa a wata mai zuwa.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal