Badakalar tauye hayakin motocin Volkswagen
September 30, 2020Talla
Shari'ar na zama ta farko da ake dauka a matsayin babban laifi na cin amana a Jamus game da tabargazar da ta faru shekaru biyar da suka wuce wanda ya janyo wa rukunin kamfanonin Volkswagen hasarar samar da euro biliyan 32 wajen biyan tara da kuma wasu hakkoki domin yin sulhu.
Rupert Stadler da sauran mutane uku da ake zargi, ana tuhumarsu ne da zamba cikin aminci da tafka karya kan hakikanin hayakin da motocin ke fitarwa da kuma tallata motocin kan tafarkin karya.
Kotun Munich da za ta gudanar da shari'ar za ta yi zama 176 na sauraron shari'ar wadda za ta dauki tsawon lokaci zuwa watan Disambar shekarar 2022.