Janar Babangida na so a sake fasalta Najeriya
June 27, 2017Fitowa fili da tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya ya yi na bayyana cewa bai ga laifi na sake wa Najeriyar fasali ba a wannan lokaci wanda ya biyo bayan dadewa da wasu sasassan Najeriya irin na kudu maso gabashin kasar suka yi da ke kama da shagube ga wasu sassan kasar. Koda a lokacin taron kasa da aka yi a 2014 a Najeriya sai da wannan batu ya taso, inda aka watse ba tare da cimma wata matsaya ba.
Tuni dai manyan jamiyyun Najeriya suka bayyana goyon bayansu a kan sauye-sauye amma ba batun raba kasa ba kamar yadda wasu matasan sassan kasar suka ambato da ya haifar da tada jijiyar wuya. Suma dai wasu daga jam'iyyar PDP mai adawa sun sanar da nuna goyon bayansu ga wannan batu na kawo gyara amma ba wai raba kasar ba.
Ko da yake Janar Babangida da ya bayyana goyon bayyansa ga masu kokarin a gudanar da sauye-sauye a Najeriya ya ci kashedi ga masu tada fitina da su sani cewa yaki fa ba wasa bane, abinda ya sanya suma daga nasu bangare shugabannin kungiyoyin kwadagon Najeriyar bayyana na su ra'a inda suka watsi da duk wani mai son tayar da fitina.
A yayin da gwamnatin Najeriya ke kokari na dinke duk wata kafa ta fitina ga masu kiraye-kiraye na a raba kasar, har zuwa yanzu babu cikakken bayani a kan shin wa ce hanya za a bi in ma har za a sakewa Najeriyar fasali da mafi yawan masu neman a yi hakan ke hasashen rage wa gwamnatin tsakiya karfi a tsari na shugaba mai cikakken iko.