1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta janye dakarunta daga Siriya

Abdul-raheem Hassan
December 20, 2018

Gwamnatin Amirka karkashin Shugaba Donald Trump ta bayyana shirin za ta janye dakarunta daga Siriya lamarin da ya haifar da cece-kuce tsakanin 'yan siyasa na Amirka.

https://p.dw.com/p/3APyJ
Syrien Krieg | Zerstörung in Aleppo
Hoto: Getty Images/AFP/A. Watad

Gwamnati Amirka ta sanar da fara janye dakarun kusan dubu biyu daga kasar Siriya cikin kwanaki 60 zuwa 100, matakin dai ya biyo bayan sakon twitter da Shugaba Donald Trump ya wallafa cewa sojojin sun gama da mayakan IS a Siriya.

Sai dai matakin na cin karo da adawar manyan sojojin Amirka ciki har da sakataren harkokin tsaron kasar, masanan na ganin janye dakarun Amirka a Siriya da gaggawa alamar yaudara ce ga mayakan Kurdawa.

Dama dai kasashe kamar Rasha na aza ayar tambaya zaman dakarun Amirka a Siriya ba bisa ka'ida ba, tare da zargin Washington da yi wa  zaman lafiya zanagon kasa a Siriya.