1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janye Sojin Spain daga Iraqi

April 19, 2004

Janye sojin Spain daga Iraqi na Neman kawo rarrabuwar kawunan kasashen Turai

https://p.dw.com/p/BvkZ
Tankin yakin kasar Spain a sansanin su dake kusa da Najaf a Iraqi
Tankin yakin kasar Spain a sansanin su dake kusa da Najaf a IraqiHoto: AP

Tun bayan da sabuwar gwmnatin Spain ta sanar da janye sojojin ta daga Iraqi nan da ranar 30 ga watan Yuni Idan har majalisar dinkin duniya bata karbi ragamar al´amura a kasar ta Iraqi ba, wanda yake neman kawo rarrabuwar kawunan kasashen turai, shugabanni da kuma manazarta ke ta sharhi akan makomar wan nan al´amari .

Rahotanni sun bayyana cewa janyewar ta sojojin Spain wani kalubale ne da zai haifar da gagarumin gibi ga dakarun sojin hadin gwiwar da Amurka kewa jagoranci a Iraqi .

A waje daya kuma Poland na nazarin hanyar da ya kamata a cike gurbin na sojojin Spain,ko da yake tace bata da niyyar kara yawan sojojin ta a can .

Kasar Spain dai ita ce kasa ta biyu dake da mafiyawan dakarun soji a Iraqi da yawan su ya kai 1,300.

A jawabin sa ga ´yan jaridu,sabon shugaban kasar na Spain Luis Zapatero ya sanar da janye sojojin kasar daga Iraqi nan bada jimawa ba don cika alkawarin da yayiwa al´umar kasar a yakin neman zabe.

A waje daya kuma rahotanni sun bayyana cewa kasar ta Poland na dakon kudirin majalisar dinkin duniya akan wannan matsayi da ake ciki,ko dai ta bada dama ga kasashen kawance su kara yawan dakarun su dake cikin sojin hadin gwiwar ko kuma su karfafa kudirin su ga gudunmawar sojin da suka bayar .

Rahotanni sun cigaba da cewa, baya ga dakarun ta su kimanin 1,300 kasar Spain din har ila yau ita ce ke jagorancin dakarun sojin El Savador da Jamhuriyar Dominican da kuma Hunduras wadanda ke da dakaru 1000 a Iraqin.

To sai dai baá fayyace ba ko su ma kasashen zasu janye nasu sojojin ne ko kuma a´a. Ala ayi-halin dai janyewar da Spain take so tayi daga Iarqi ya dagulawa kasashen kawancen al´amura musamman ma kasar Amurka

A wani bangaren kuma Prime Ministan Australia John Howard ya soki lamirin kasar Spain na janye sojojin ta daga Iraqi inda yake cewa hakan ba zai haifar da komai ba sai kara yawan yan taádda masu kai hare haren kunar bakin wake

Haka kuma an Ruwaito Ministan harkokin wajen kasar ta Australian Alexander Downer,na cewa ya tattauna da Jakadan Spain a kasar inda ya gabatar masa da rashin jin dadin su

Shi dai sabon PM kasar Spain Luis Zapatero mai shekaru 43 da haihuwa wanda ya kada tsohon P/M kasar Jose-Mario Aznar a zaben da aka gudanar a kasar a ranar 14 ga watan Maris,kwanaki uku bayan harin Bom din nan na Madrid,shugaban ya yi alkawarin dawo da sojojin kasar sa gida domin kamar yadda yace babu wata hujja a yakin da Amurka take a Iraqi .