1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Japan: Jiragen sama na sojin ruwa ya yi hatsari

April 21, 2024

Jiragen sama masu saukar ungulu guda biyu na rundunar sojin Japan sun yi hatsari a lokacin da suke atisaye a tsibirin Izu.

https://p.dw.com/p/4f178
Hatsarin jiragen biyu kirar SH-60K ya auku ne a lokacin da suke atisaye a Japan
Hatsarin jiragen biyu kirar SH-60K ya auku ne a lokacin da suke atisaye a JapanHoto: Japan Maritime Self-Defense Force via AP

Ministan tsaron Japan ya ce mutum daya ya rasa ransa yayin da sauran fasinjoji bakwai suka yi batan dabo sakamakon fadawa cikin teku da Jirage sama masu saukar ungulu guda biyu na rundunar sojin ruwa na kasar suka yi.

Hatsarin jiragen biyu kirar SH-60 ya auku ne a lokacin da suke atisaye a jiya Asabar a Torishima da ke tsibirin Izu a kudancin gabar ruwan Japan.

Ministan tsaron kasar, Minoru ya bayyanawa manema labarai cewa, an kaddamar da fara binciken kan sanadiyar aukuwar hatsarin wanda ake hasashen ta yi wu jiragen sun yi kusa da juna ne sosai, inda suka yi taho-mu gama.

Tuni kuma jami'an kula da tekun suke ci gaba da neman sauran fasinjojin da suka bata. Shugaban rundunar sojin kasar Japan Yoshitaka Sakai ya ce yana kyautata zaton babu hannun wata kasa a cikin hatsarin.