1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murabus din shugaban 'yan sandan Japan

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 25, 2022

Shugaban hukumar 'yan sandan kasar Japan, Itaru Nakamura ya sanar da cewa zai yi murabus, saboda gaza kare firaministan kasar Shinzo Abe da wani ya bindige shi har lahira.

https://p.dw.com/p/4G3uf
Japan | Itaru Nakamura
Shugaban Hukumar 'yan Sanda ta Japan Itaru NakamuraHoto: Hiroto Sekiguchi/Yomiuri Shimbun/AP Photo/picture alliance

Nakamura dai shi ne jami'in dan sanda mafi girman mukami a Japan na farko da ya sauka daga mukaminsa, tun bayan afkuwar kisan gillar na Abe da ya girgiza kasar. Yayin wani taron manema labarai da ya gudanar, Nakamura ya bayyana sakamakon bincike kan kisan na Abe da ya nuna cewa an gaza ba shi kariya daga bayansa saboda rashin yin tunanin yiwuwar kai masa hari. Da ma tuni Nakamura ya bayyaana nadama kan gazawar 'yan sanda wajen bai wa Abe kariya, yayin gangamin yakin nemana zaben da aka harbe shi har lahira a wajen.