1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan na son sulhunta Iran da Amirka

Ahmed Salisu
December 9, 2019

Firaministan Japan Shinzo Abe ya ce kasarsa ta himmatu wajen ganin ta sulhunta Amirka da Iran wadanda ke suka dau tsawon lokaci suna takaddama.

https://p.dw.com/p/3UUVp
Japan Kabinettsumbildung Shinzo Abe
Hoto: picture-alliance/AP/Yomiuri Shimbun/S. Izumi

Firaminisan Japan Shinzo Abe ya bayyana a wannan Litinin din cewar kasarsa ta fara shirye-shirye na tarbar shugaban Iran Hassan Rouhani sai dai bai yi karin haske kan takaimaiman lokacin da Rouhanin zai je Japan din ba.

Firaminista Abe ya ce kokarin da kasarsa ke yi na shiga tsakani kan rikicin da ake yi tsakanin Amirka da Iran kan shirin nukiliyar Tehran ne ya sanya shi gayyatar Shugaban Rouhani din don su tattauna.

A matsayinta na guda daga cikin manyan aminan Amirka, Japan ta ce hakki ne da ya rataya a kanta ta daidaita bangarorin biyu da ke zaman 'yan marina don a wanzar da zaman lafiya tsakaninsu tare da daidaita lamura a yankin gabas ta tsakiya.