Tuna ranar bala'in Fukushima
March 11, 2021A wannan Alhamis Japan ke cika shekaru goma cur da aukuwar fashewar tukwanan makamashin nukiliyar Fukushima a sakamakon munmunar girgizar kasa da Tsunami da suka afkawa yankin arewa maso gabashin kasar. Girgizar kasa mai karfin maki tara a ma'aunin Rishta, ta haifar da igiyar ruwan Tsunami da ta shafe birane tare da halaka mutane sama da dubu goma sha takwas a yayin da wasu kusan rabin miliyan suka rasa matsuguninsu.
Shekaru goma da aukuwar fashewar da Tsunamin, jama'a na ci gaba fama da abin da ya biyo bayan wannan bala'in. Firaiministan kasar, Yoshihide Suga ya jagoranci taron tuna ranar, inda aka yi tsit na minti guda kafin jawabin Suga, a ciki, ya ce ba za su taba mantawa da ranar da kuma darussan da suka koya a ranar da Japan ta tsinci kanta cikin yanayi na tsananin jimami ba.