Japan za ta shirya gasar Olympics ta 2020
September 8, 2013Jacques Rogge shugaban kwamitin wasannin na Olympics shi ne ya bayyana sunan ƙasar ta Japon a matsayin ƙasar da za ta tsara wasanin a wani zaman taron da kwamitin na Olympics ɗin ya yi a Buenos Aires. A ƙarshen ƙidayar ƙuri'un da aka yi birnin Tokyo ya samu kuri'u 60, kana Istanbul na da 36, bayan tun da farko dai an riga aka fitar da birnin Madrid tun a zagayen fari.
Wannan dai shi ne karo na biyu da ƙasar ke shirya wasannin bayan wanda ta tsara a shekara ta1964,sai dai kuma a ƙasashen Spain da Turkiya waɗanda suka sha kaye a takarar an yi tsit kamar a yin mutuwa.Tun da farko dai an yi tsamanin Japan ɗin ba za ta samu nasarar ba saboda lamarin da ya afku a ƙasar a shekara ta 2011 na hatsarin tashar nukiliya ta Fukushima.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman