Jaridun Jamus: Aljeriya za ta shiga tsakani
October 6, 2023Jaridar die Zeit ta ruwaito ministan harkokin wajen Aljeriya Ahmed Attaf yana na cewa ya yi damarar zuwa Nijar. Dama dai tun bayan juyin mulki a Nijar, kasar Aljeriya ta ba da kanta a matsayin mai shiga tsakani, amma yanzu da alamu gwamnatin mulkin soja a Yamai ta amince da wannan tayin. Ma'aikatar Harkokin Wajen Aljeriya ta sanar da cewa, a yanzu an kai ga warware rikicin cikin lumana da siyasa. A cewar jaridar duk da cewa hukumomin sojan Nijar ba su ce komai ba kan wannan labari, amma kuma batun na Aljeriya ba abunda za a musanta ba ne.
Jaridar die tageszeitung ta ce arewacin Mali na kara fada wa cikin yaki, fada na ci gaba da bazuwa tsakanin sojojin gwamnatin Mali da 'yan tawayen Abzinawa a kokarin kwace sansanonin sojin da Faransa da Majalisar Dinkin Duniya suka bari. Kungiyoyin 'yan ta'adda masu kishin Islama kuwa wadanda ke kai wa fararen hula hari su ma suna kara shiga cikin lamarin dagula tsaro a Mali. Yakin da ake gwabzawa tsakanin sojojin Mali da 'yan tawayen Abzinawa a arewacin kasar ya sake barkewa, kuma gwamnatin kasar na kara samun kanta cikin kunci musamman kazamin yakin da ake yi a tsakanin manyan lardunan Timbuktu da Gao.
Ita kuwa Der Spiegel cewa ta yi shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi na son sake tsayawa takara a karo na uku a zaben shugaban kasar da za a yi a watan Disamba. Tsohon Janar din mai shekaru 68 ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a gidan talabijin. Tashoshi masu goyon bayan gwamnati sun nuna hotunan jama'a da suka yi ta murna bayan jawabin da ya yi ta fuskar allunan talla a garuruwan Masar. Ko da shike Al-sisi ya kawo ci gaba a wani bangaren gina kasar, amma yana mulkin kama-karya ne, kuma kasar da ta fi yawan al'umma a arewacin Afirka, na fama da matsananciyar matsalar tattalin arziki, da hauhawar farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar kudin kasar.
Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi tsokaci kan sabanin kasar Tunisiya da Tarayyar Turai, inda ta ce kudin Saudiyya a maimakon "sadaka" daga Turai. Ita dai kasar Tunisiya ta ki karbar taimakon kudi daga EU. Jaridar ta ce ya kamata Tunisiya ta zama abokiyar kawancen Turai da aka fi so a yaki da kwarar bakin haure. Amma shugaba Kais Saïed ya ki amincewa da kudaden da EU ta bayar, yana mai kiran ta "sadaka". Da alama shugaban kasar ya fusata musamman da kusan Euro miliyan 67 da kungiyar EU ke son mika wa Tunisia watanni biyu da rabi bayan sanya hannu kan wata yarjejeniya. goyon baya wajen dakile yan gudun hijira ba bisa ka'ida ba. Tunisiya a shirye ta ke ta ba da hadin kai, amma ba ta son "rashin mutunci," in ji sanarwar da fadar shugaban kasar Tunisiya ta fitar.