1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jinkirta samar da allura a Afirka

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
June 18, 2021

Hankalin jaridun a wannan makon ya koma kan jinkiri wajen samar wa da kasashen Afirka allurar riga-kafin corona.

https://p.dw.com/p/3vAzi
Mali Frankreich beendet die Operation „Barkhane“
Sojojin Faransa sun fice daga kasar Mali, bayan sojojin Malin sun sake karbe mulkiHoto: AP Photo/picture alliance

A labarin da jaridar Die Tageszeitung ta rubuta mai taken "Macron ya sanar da shirin janye dakarunsa daga Mali." Jaridar ta ce shugaban kasar ta Faransa na son kawo karshen aikin rundunar  yaki da ayyukan tarzoma ta Barkhane a yankin Sahel. Tun bayan sojoji suka sake kifar da mulkin Mali a baya-bayan nan ne dai, Faransar ta sanar da dakatar da ayyukan sojojinta a wannan kasa da bisa dukkan alamu ta rasa alkibla a siyasance. Ba zato babu tsammani ne dai shugaba Emmanuel Macron ya ayyana sauya fasalin aikin dakarun da suka jima su na aikin yakar mayakan tarzoma  a Mali, wadanda aka kara yawansu a baya-bayan nan zuwa 5,100.

Cikakkun bayanai dangane da yadda Faransar za ta janye wadannan sojoji na ta zai bayyana ne kadai a karshen wannan wata na Yuni da muke ciki.Tun a farkon shekara ta 2013 nedai, Faransar ta shiga yaki da masu tsananin kishin addini a Mali, inda da ta samu nasarar fatattakarsu daga arewacin kasar in da a lokacin suke da madafan iko. A shekarar 2014 ne kuma aka sanyawa randunar Barkhane, wadda ke yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Sahel baki daya.

Coronavirus | Impfstoff von Johnson & Johnson
Kasashen Afirka na fuskantar karancin allurar riga-kafin coronaHoto: MiS/imago images

"Allurar riga-kafin da aka yi wa Afirka alkawari, na iya zuwa a makare." Da haka ne jaridar Neue Zürcher Zetung ta bude sharhin da ta wallafa dangane da allurai kalilan da aka kai nahiyar, idan aka kwatanta da yadda coronar ke kara yaduwa a Afirkan. A cewar jaridar kashi daya ne kacal na yawan al'ummar Afirkan biliyan daya da miliyan 300, suka samu cikakkiyar allurar riga-kafin COVID 19. Hukumar Kula da Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO, ta ayyana cewar kasashen nahiyar da dama ba za su cimma muradun da aka sanya a gaba na yi wa mafi yawan al'umma allurar nan da watan Satumba ba.

Dalili kuwa shi ne, kashi biyu ne kacal na yawan allurar da ake yi a fadin duniya, ya isa nahiyar ta Afirka. A wannan wata na Yuni dai, alkaluman wadanda suka kamu da cutar corona a Afirka sun karu zuwa kaso 25 cikin 100, idan aka kwatanta da makonnin baya. A yayin da kasashe da dama ke fama da sababbin nau'o'in cutar, akwai rahotannin barkewar ta a zagaye na uku, batun da ko kadan nahiyar ba ta yi wa tanadi ba. Kasashe masu karfin tattalin arziki na G7, sun sanar da samar da biliyoyin allurar riga-kafin kuma mafi yawa za su tafi Afirka.

Impfkampagne in Südafrika
Afirka ta Kudu cikin halin tasku sakamakon coronaHoto: Siphiwe Sibeko/AP Photo/picture alliance

Ita ma jaridar Die Tageszeitung ta yi tsoakaci ne dangane da halin da Afirka ta Kudu ta tsinci kanta dumu-dumu cikin zagaye na uku na annobar ta COVID-19. Sama da shekara guda ke nan da kasar mai bunkasar tattalin arziki a baya, ke cikin wadi na tsaka mai wuya na karuwar marasa aikin yi, baya ga kokarar ministan lafiya bisa zargin rashawa. 16 ga watan Yuni na zama ranar matasa kuma ranar hutu na kasar ta Afirka ta Kudu, wanda ke zama ranar tunawa da matasa 200 da suka rasa rayukansu a Soweto da ke kusa da birnin Johannesburg.

A ranar 16 ga watan Yunin shekarar 1976 ne dai, dalibai bakar fata wajen dubu 20 suka gudanar da bore kan halin da matasa da yara bakar fata matalauta suke ciki a Afirka ta Kudu. Nan take 'yan sanda suka buda musu wutar da ta janyo asarar rayukan matasa 200, ban da dubu hudu da suka jikkata. Sai dai matasan na yanzu na ganin cewar babu dalilin bukin tunawa da wannan rana, a daidai lokacin da corona ta shiga shekara ta biyu na jefa rayuwarsu cikin halin kaka-ni-ka-yi.