1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juyin mulkin Burkina Faso ya dauki hankalin jaridun Jamus

Usman Shehu Usman
February 11, 2022

Jaridar der Freitag ta ce a yammacin Afirka biyo juyin mulkin da aka yi a Burkina Faso, hakan na nuna cewa kasar Faransa na kara rasa tasiri a wannan yanki.

https://p.dw.com/p/46uFA
Burkina Faso | Hoton  Lt. Col. Paul Henri Sandaogo Damiba
Hoto: Sophie Garcia/AP Photo/picture alliance

Jaridar der Freitag na mai cewa a bara an yi juyin mulki a Chadi, Mali da Guinea. Yanzu, a ranar 24 ga Janairu, an mayar da mulki ga gwamnatin soja a Burkina Faso ma. Abin da ya fi daukar hankali shi ne wadannan kasashe ne wadanda ya zuwa yanzu suna da alaka da Faransa. Baya ga Guinea, babban dalilin juyin mulkin dai shi ne gazawar hadin gwiwar soji da tsohuwar gwamnatin mulkin mallaka a yakin da ake yi da kungiyoyin jihadi. A Burkina Faso, masu da'awar jihadi sun fatattaki sojojin kasa daga yankunan arewaci da gabashin kasar tun daga shekarar 2016. 

Ita ma dai Jaridar Süddeutsche Zeitung , labarinta ya karkata ne a bisa raunin dangantakar Faransa da kasashen da ta yi wa mulkin mallaka. Inda jaridar ta fara tsokaci da cewar: Kasar mu ce, wato ikirarin 'yan kasar Mali. Yawancin mutanen Mali sun yarda cewa muddin Faransawa na can, to babu abin da zai gyaru. Sun fi son yi wa masu juyin mulki jinjina. A tsakiyar Bamako, babban birnin kasar ta Mali, an ga dubban mutane na ta jerin gwano, wasu suna kona tutar Faransa, wasu na sanye da riguna masu launin kasar Mali da na Rasha, wasu kuma na sanye da riguna masu dauke da hoton shugaban kasar Assimi Goïta, suna ta wakokin zagin Faransa.

Mali, Gao | Jirgin sojin Barkhane na Faransa
Hoto: Frédéric Speich/LA PROVENCE/PHOTOPQR/MAXPPP/dpa/picture alliance

Sai kuma Kasar Sudan ta Kudu, inda jaridar Der Tagesspiegel ta yi sharhi tana mai cewa fatan zaman lafiya a yanzu. Jaridar ta ci gaba da cewa ko da shekaru hudu bayan kawo karshen yakin basasa a hukumance, rikicin kabilanci a Sudan ta Kudu na ci gaba da haifar da tashin hankali. Dubban mutane suna zaune a sansanonin 'yan gudun hijira kuma suna fama da yunwa. Kuma tun a bara ne komai ya canza. Inda tashin hankali ya mamaye yammacin Equatoria, kwatsam kuma babu kakkautawa kamar guguwar tsunami da ke barin yanke kauna da tarkace a farke. 

Gasar AFCON Sadio Mane na Senegal rike da kofin zakarun Afrika
Hoto: Charly Triballeau/Getty Images/AFP

Neues Deutschland Litinin din wannan makon ta kasance ranar hutu a Senegal. Dalili kuwa shi ne kungiyar kwallon kafar kasarsu ta lashe gasar cin kofin  Afirka a karon farko. Tun gabanin buga wasan karshe tsakanin Masar da Senegal, duk birnin Dakar ya cika makil, to fa bayan da Sadio Mane ya rama fenariti a wasan da suka doke Masar da ci 4-2, murna a kan titunan Senegal ba iyaka. An barke da murna, jama'a na kuka da farin ciki. Motoci an yi musu ado da tutoci masu launin kore-rawaya da ja, inda suka bi ta cikin birni suna ta rawa babu kakkautawa. A tsakanin, yara da matasa sun kasance cikin launuka na tutar kasar. Don haka ba mamaki shugaba Macky Sall ya ayyana ranar litinin a matsayin hutu ga al'ummar da suka yi nasara don a samu damar yin bukuwan murnar lashe gasar kwallon Afirka. Can da tsakar rana aka yi babban tarba da tawagar ta iso gida.