1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Rufe sansanin 'yan gudun hijira a Kenya

Mohammad Nasiru AwalMay 13, 2016

Dadaab da ke kan iyakar Kenya da Somaliya shi ne sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya inda 'yan Somaliya kimanin dubu 600 suka samu mafaka.

https://p.dw.com/p/1InZs
Kenia Das Flüchtlingslager Dadaab
Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Za mu fara sharhi da labaran jaridun na Jamus game da nahiyarmu ta Afirka da jaridar Franfurter Allgemeine Zeitung wadda a wannan makon ta leka kasar Kenya tana mai cewa Kenya za ta rufe sansanin 'yan gudun hijira na kan iyaka kana za ta kori 'yan gudun hijirar Somaliya.

Ta ce Kenya za ta rufe sansanin Dadaab da ke zama sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya kana ba za ta kara daukar 'yan gudun hijira daga Somaliya ba. Gwamnati ta ce dalilan tsaron kasa suka sa ta dauki wannan mataki da tuni ya fara shan suka daga kungiyoyin agaji. Jaridar ta ce sansanin na Dadaab ya zama wani yanki na uku mafi girma a kasar ta Kenya idan aka kwatanta da yawan mazauna ciki, da ke rashin kusan dukkan abubuwan more rayuwa, kuma 'yan tarzomar kungiyar al-Shabaab na amfani da shi tana daukar matasa suna kai hare-hare a Kenya.

Mutane dubu 600 za su bar manyan sansanoni biyu a Kenya inji jaridar Der Tagesspiegel tana mai cewa baya ga sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab da ke kan iyakar Kenya da Somaliya, mahukuntan birnin Nairobi za su kuma rufe sansanin Kakuma inda 'yan gudun hijira daga kasashe makwabta masu fama da yake-yaken basasa irinsu Somaliya da Sudan da ma kasashen Habasha da Eritriya suka samu mafaka. Sansanin Dadaab da aka kafa a shekarar 1991 na zama mahaifar daukacin matasan na Somaliya da ke a Kenya.

Daurin rai da rai ga wasu sojojin Burundi

A labarinta mai taken "Matakin ba sani ba sabo ga wadanda suka yi yunkurin juyin mulki" jaridar Die Tageszeitung ta leka kasar Burundi ne tana mai cewa hukuncin daurin rai da rai ga sojojin da a bara suka yi yunkurin yi wa shugaban Burundi Pierre Nkurunziza juyin mulki.

Burundi am Abgrund
Zanga-zangar adawa da Shugaba Nkurunziza a baraHoto: Igor Rugwiza

Ta ce shekara guda ke nan daidai bayan wani yunkurin juyin mulki a Burundi da bai yi nasara ba, lokacin da wani sashe na sojojin kasar ya ce ya sauke shugaba Nkurunziza daga kan madafun iko, amma kwanaki biyu baya sojojin suka lashe amansu. A wannan makon babbar kotun kasar ta tsananta hukunci a kan jami'an soji da na 'yan sanda 28. Wannan shari'ar dai na zama wata muhimmiyar alama ko Nkurunziza bayan murkushe dukkan masu tada kayar baya da wadanda suka kalubalanci zabensa karo na uku a bara, zai nemi hanyar sulhu. Tun bayan yunkurin juyin mulkin dai kan rundunar sojin kasar ya rarrabu.

Annobar cutar shawara saboda sakacin hukuma

Angola Luanda Impfkampagne Gelbfieber
Layin karbar allurar riga kafin shawara a birnin LuandaHoto: DW/B. Ndomba

Sakacin gwamati ya janyo karuwar yawan masu fama da shawara a kasar Angola inji jaridar Süddeutsche Zeitung. Ta ce kowane bako da zai shiga kasar Angola dole sai ya nuna shaidar cewa an yi masa allurar riga kafin cutar shawara ko kuma a hana shi shiga kasar. To sai dai gwamnati ta gaza wajen ba wa al'ummarta kariya daga kamuwa da wannan cutar. Jaridar ta ce kalilan ne daga cikin 'yan kasar ta Angola aka yi wa allurar riga kafin cutar ta shawara yayin da akasarin 'yan kasar ciki har da mazauna unguwannin da ke wajen babban birnin kasar wato Luanda ke kamuwa da kwayoyin cutar, kuma annobar na yaduwa a yankuna da dama na kasar ta Angola.