1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Najeriya a mahangar jaridun Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar RGB
October 14, 2022

Babban zaben Najeriya na 2023 da rikicin siyasar kasar Burkina Faso su suka fi daukar hankulan jaridun Jamus a wannan makon.

https://p.dw.com/p/4IDVq
Jaridun Jamus
Sharhunan Jaridun Jamus kan nahiyar AfirkaHoto: picture-alliance/united-archives/mcphoto

Jaridar die tageszeitung wadda ta rubuta sharhinta mai taken: "Kada gangar siyasa a Najeriya, takarar shugabancin kasa tsakanin tsofaffi." Jaridar ta ce: Manyan jam'iyyun siyasar Najeriya biyu, sun tsayar da tsofaffi takarar shugabancin kasa a zaben shekara ta 2023 da ke tafe. Sai dai rikicin cikin gida na sanya fargabar gangamin yakin neman zabe ka iya zama na a mutu ko a yi rai. 

Yayin da ya rage watanni kalilan a gudanar da babban zabe a Najeriya, yanayin siyasar kasar da ke da yawan al'umma miliyan 217 na kara hargitsewa. Shugaban kasar mai barin gado Muhammadu Buhari bai tabuka wani abun azo a gani ba, bayan wa’adin mulki har biyu. Hakan na zaman jan aiki a gaban duk wanda ya gaje shi bayan zaben watan Fabarairun shekara ta 2023 da ke tafe. Babbar jam'iyyar adawa ta PDP da ta fara mulkar kasar bayan komawa turbar dimukuradiyya a shekara ta 1999 na fatan komawa kan karagar mulki. 

Sai dai kuma lokaci na kure mata, wajen sulhunta rikicin cikin gida da take fama da shi wanda kuma ya dauki hanyar ta'azzar rikicin kabilanci a Najeriyar da ke da tarin kabilu. Jam'iyar ta PDP ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriya Atiku Abubakar da ya sha tsayawa takara amma ya gaza kai bantensa. An tsammaci mai shekaru 75 Musulmi da ya fito daga yankin arewacin Najeriyar zai zabi Ezenwo Wike mai shekaru 54 Kirsita daga kudancin kasar a matsayin mataimaki. 

Sai dai kuma Abubakar ya ayyana Ifeanyi Okonwa mai shekaru 64 daga yankin kudancin Najeriyar a matsayin mataimakinsa abin da ya sanya Wike ke ganin ya kamata PDP ta tsayar da wani dan takarar shugaban kasa na dabam. A ganinsa, kasancewar Buhari Musulmi daga arewacin Najeriya, bai kamata a sake samun Musulmi daga Arewa a matsayin shugaban kasa ba. 

Kombobild | Hauptkandidaten für die nigerianische Präsidentschaftswahlen Bola Tinubu und Atiku Abubakar
Bola Tinubu da Atiku Abubakar

A nata bangaren jam'iyyar APC mai mulki ta Shugaba Buhari na maraba da rikicin cikin gidan na babbar jam'iyyar adawar, APC ta tsayar da Bola Tinubu tsohon gwamnan jihar Lagos da ke zaman cibiya kasuwancin kasar kana Musulmi daga kudancin kasar a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasar na shekara ta 2023 da ke tafe, inda shi kuma ya zabi Kashim Shettima tsohon gwamnan jihar Borno Musulmi daga Arewa a matsayin mataimakinsa. 

A hannu guda kuma, akwai tsofaffin gwamnoni biyu da suka yi mulki a karkashin jam'iyyar PDP da kuma ke da matukar tasiri da suma suka tsaya takara a wasu jam'iyyun na dabam. Rabiu Kwankwaso na jam'iyyar NNPP da kuma Peter Obi na jam'iyyar LP. Wannan ya sauya yanayin siyasar kasar da ya kasance tun daga shekara ta 1999 inda ake damawa a tsakanin manyan jam'iyyu biyu kacal. 

Juyin mulki karo na biyu cikin shekara guda, inji jaridar Neues Deutschland. Jaridar ta ce, ta yiwu shugaban kasa na riko Ibrahim Traoré ya zama sabon fata ga al'ummar kasar Burkina Faso. Ta ce musamman matasa na yi wa Traoré kallon sabon gwarzo da ka iya magance matsalolin kasar, sai dai kuma ana kallon juyin mulkin a matsayin tawaye ga Faransa da ta yi wa Burkina Faso mulkin mallaka. Da dama na alakanta Traoré da tsohon shugaban gwagwarmayar kwatar 'yancin kasar Thomas Sankara. Dukkaninsu sun dare kan karagar mulki suna da shekaru 34. Traoré ya sake yin juyin mulki a Burkina Faso, watanni takwas bayan takwaransa Paul-Henri Sandaogo Damiba ya yi juyin mulki. Sojojin na ikirarin kokarin shawo kan matsalolin kasar da suka hadar da na 'yan ta'adda da ke da nasaba da kungiyoyin ta'adda na IS da al-Qa'eda.

Lage in Burkina Faso
Sojoji sun yi Juyin mulki a Burkina FasoHoto: Radiodiffusion Télévision du Burkina/AFP

Bari mu karkare da sharhin jaridar Die Welt mai taken: "Karuwa tasirin Putin a Afirka." Ta ce: Bayan juyin mulki a Burkina Faso, sojan da ke goyon bayan Rasha ya dare kan madafun iko. Jaridar ta ce, bisa al'ada ba a samun dandazon masu goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki. Sai dai ga sabon jagoran mulkin soja na Burkina Faso Ibrahim Traoré abun ba haka yake ba. Duk da cewa an yi tir da juyin mulkin kamar yadda aka tsammata, daga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin Tarayyar Afirka da Tarayyar Turai da kuma Kungiyar Habbaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma, amma Rasha ta yi masa fatan alkhairi. 

Sojojin hayar Rasha na Wagner da ke da alaka da fadar Kremlin, sun yi masa murnar samun damar kwace iko. Ga dukkan alamu fadar ta Kremlin, ta samu abokin huldar da ta yi fatan samu lokacin wanda Traoré ya gada wato Paul-Henri Sandaogo Damiba da ya kwace mulki daga hannun gwamnatin farar hula a farkon wannan shekara. Tuni dai aka hango magoya bayan Traoré dauke da tutocin Rasha kana shi ma ya bayyana karara cewa, Mosko ka iya zama sabuwar abokiyar hulda.